1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon: Hariri ya ce dan kansa ya yi murabus

Mouhamadou Awal Balarabe | Salissou Boukari
November 13, 2017

Firaministan Lebanon mai murabus Saad Hariri ya karyata zargin da ake yi na cewa Saudiyya ce ta tilasta masa yin murabus tare da hanashi zirga-zirga yadda yake so.

https://p.dw.com/p/2nWh5
Saudi Arabien Ex-Premier Hariri kündigt Rückkehr in den Libanon an
Firaministan Lebanon mai Marabus Saad HaririHoto: Reuters/M. Azakir

Shi dai Saad Hariri mai shekaru 47 da hihuwa ya ce ba wanda ya ke hana masa rawar gaban hantsi a Riyadh saboda tamkar gida ne a gareshi: A wannan birni a ka haifeshi, a nan ne ya fara tafiyar da harkokin kasuwancin mahaifinsa lokacin da ya taso, sannan kuma yana kewaye da sauran 'yan Sunni wadanda akwai kyakyawar alaka tsakaninsu. Sai dai a kasar Lebanon hamshakin dan kasuwan na da makiya da dama, musamman ma a tsakanin kungiyar Hezbollah ta 'yan Shi'a, wadda Saad Hariri ya soki manufofinta.

"A shekarun da suka gabata, abin takaici Hezbollah ta yi nasarar yada akidunta a Lebanon ta hanyar amfani da tsinin bindiga. Wadanda suke tafiyar da ita da ke daukar Hezbollah a matsayin kungiyar gwagwarmaya, su na amfani da ita wajen yakar 'yan'uwanmu a Siriya da Yemen da kuma Lebanon."

Libanon Hisbollah Hassan Nassrallah
Jagoran kungiyar Hezbollah na kasar Lebanon Hassan Nassrallah ya zargi Sadiyya da tilastawa Saad Hariri yin murabusHoto: picture-alliance/dpa

Ita dai Hezbollah da ke da goyon bayan Iran na shiga ana damawa da ita a rikice-rikicen da kasashen Larabawa ke fuskanta, lamarin da Firaministan na Lebanon Mai murabus ya nuna takaicinsa a kai. A takaice dai Saad Hariri na goyon bayan Saudiyya a sa-in-sa da take yi da Hezbollah a Yemen da Siriya da Bahrein da Iraki. Hariri yana da fili a gefen Saudi Arabia.

Mahaifinsa, Rafik Hariri, ya tafi Saudiyya a matsayin matashi kuma ya gina ginin dubban miliyaoyi a can. Ya koma Labanon a shekarun 1990 kuma ya kasance firaministan kasar sau biyu. Ba da daɗewa ba bayan da ya yi murabus a shekara ta 2005, an kashe Rafik Hariri, yayin da aka dana masa bama-bamai, kuma kimanin mutane 23 ne suka mutu a lokacin kuma harin ya girgiza ƙasar. Saad al-Hariri ya fara bautar mahaifinsa. Daga tsakanin 2009 zuwa 2011, shi ne Firayimista na farko har lokacin da Hezbollah ta janye daga gwamnatin hadin kai. Ta bayyana a fili, saboda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da takardar izini ga 'yan kungiyar Hezbollah da kuma sanya su alhakin kisan gillar Rafik Hariri. Babban Sakataren Hezbollah Hassan Nasrallah ya yi watsi da wadannan zarge-zarge.