1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen rikicin Libiya

January 15, 2015

Majalisar dinkin duniya ta fara tattaunawa da bangarorin da ke gaba da juna a Libiya a birnin Genenva na kasar Switzerland da nufin kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa a kasar.

https://p.dw.com/p/1EKim
Hoto: Reuters

Zaman na Geneva dai na fatan kafa gwamnatin hadin kan kasa domin farfado da ita daga halin ha'ula'in da ta fada. Majalisar dai ta kwashe tsahon watannin kafin sake shirya irin wannan tattauna tun bayan da ta shirya irinta a watan Satumbar shekarar da ta gabata ta 2014. Wolfram Lacher na makarantar nazarin kasa da kasa da kuma al'amuran tsaro da ke nan Jamus ya yi karin haske kan asalin rikicin na Libiya yana mai cewa.....

"Juyin-juya halin Libiya ba juyin-juya hali ne da aka yi cikin ruwan sanyi ba, an yi shi ne a matsayin yakin basasa. Da gwamnatin kasar ta rushe baki dayan kasar ta rushe haka nan ma bangarorin tsaro na kasar sun bi sahun gwamnatin wajen rushewa. Masu juyin-juya halin basu da shugabanci na hadin kai, a dangane da haka gwamnatin na faduwa sai suka fara rikici a tsakaninsu. Tsakanin kabilu biyu daga nan sai suka zama kungiyoyi biyu masu gaba da juna, wannan shine kalubalen da muke fuskanta a yanzu."

Mawwallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman