1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a kafa gwamnatin wucin gadi a kasar Libiya

Binta Aliyu Zurmi MNA
February 1, 2021

A wannan Litinin bangarorin da ke gaba da juna a Libiya suka fara wani zama na kwanaki biyar a birnin Geneva na kasar Switzerland da nufin fara shirye-shiryen yadda za a mika mulki ga gwamnatin wucin gadi a Libiya.

https://p.dw.com/p/3og3h
Schweiz Genf | Gespräche zu Waffenstillstand in Libyen - Stephanie Williams
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

A taron za a fara da sauraren 'yan takara 45 da za su kara a zaben shugabannin da suka hada da tawagar mutum uku da za su shugabanci kasar da kuma Firaminista da zai ja ragamar mulkin kasar har zuwa watan Disamban bana kafin a gudanar da zaben gama gari.


Da take jawabi ga wakilai a taron, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Libiya Stephanie Williams ta yi kira ga bangarorin biyu, a matsayinsu na wakilan al'umma da su yi aiki tare domin fitar da kasar daga halin da ta shiga. 

Kasar ta Libiya na cikin wani hali na rashin tabbas tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar Ghaddafi a shekarar 2011.