1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Limamin Cocin da aka sace ya na Najeriya

November 15, 2013

Shugaban Faransa Francois Holland ya nunar da cewar limamin kiristan da aka sace a arewacin Kamaru ya na hannu masu gaggwarmaya da makamai a Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/1AIZh
French President Francois Hollande speaks during a news conference at the Slovak government building in Bratislava, October 29, 2013. Hollande is on a one-day official visit to Slovakia. REUTERS/Radovan Stoklasa (SLOVAKIA - Tags: POLITICS)
Francois HollandeHoto: Reuters

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa limamin addinin kiristan nan da aka sace a arewacin Kamaru ya na Tarayyar Najeriya yanzu haka inda ake garkuwa da shi. Da ma dai wata majiya ta bayyana wa kananin dillancin labaran Faransa AFP cewa shi limamin mai suna Georges Vandenbeusch ya na hannun kungiyar nan da aka i sani da suna Boko haram wacce ke gaggwarmaya da makamai.

A daren laraba zuwa alhamis ne aka sace Vandenbeusch a gidansa da ke wani gari da ke kan iyakar Tarayyar Najeriya da kuma kamaru. A lokacin da ya ke jawabi a zauren wani taro da aka shirya a birnin Paris, Holland ya ce wannan garkuwar ba ta rasa nasaba da fatattakar masu kaiin kishin addini da kasarsa ta taimaka aka yi a arewacin Mali.

Nan gaba kadan ne Holland zai tattauna ta wayar tarho da takwaran aikinsa na kamaru wato Paul Biya inda za su yi nazarin hanyoyi da za a bi wajen kubutar da limamin kiristan dan asalin Faransa. Shi dai shugaban na kamaru ne ya taimaka wajen ceto wasu 'yan Faransa da aka yi garkuwa da su aTtarayyar Najeriya a watannin baya.

Mawallai: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba