1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Louis Rwagasore: Yarima mai son hadin kai

July 31, 2018

Yana daga cikin wadanda ba a sani sosai ba, da suka taka rawar samun 'yanci a kasashen Afirka, amma Yarima Louis Rwagasore ya jagoranci Burundi cikin kwanciyar hankali bisa hanyar samun 'yanci.

https://p.dw.com/p/2sLXG
Louis Rwagasore: Yariman da ya jaranci hadain kai a Burundi
Louis Rwagasore: Yariman da ya jaranci hadain kai a BurundiHoto: Comic Republic

Sai dai bai amfana da aikin da ya yi ba: Firaministan na gajeren lokaci Louis Rwagasore an hallaka shi kafin Burundi ta samu 'yanci.

"Zaman lafiya, da nishadi gami da bunkasa a Burundi”: wannan ke zama fata ga Yarima Louis Rwagasore, wanda yake da tunanin samar da tattalin arziki da samun 'yancin kai cikin kwanciyar hankali.

 

Shin ya yi suna saboda jinin sarauta ne?

Gaskiya ce Louis Rwagasore ya girma da gata a matsayin yarima: shi ne babban dan Mwami Mwambutsa Bangicirenge Sarkin Barundi, sanna ya samu ilimi a daya daga cikin makarantu masu daraja da ke Ruwanda - karkashin malamai 'yan Beljiyam lokacin da Ruwanda da Burundi suke hade. Bayan karanta harkokin mulki da noma a birnin Brussels, ya gamu da sauran dalibai daga kasashen Afirka. Rwagasore ya koma gida a shekarar 1956, inda ya shiga harkokin siyasa kuma kwarjinin da yake da shi ya janyo masa farin jini.

Yariman da ya jagoranci hadin kai

Wacce hanya ya bi wajen hada kan 'yan Burundi?

Louis Rwagasore yana da dabaru na diplomasiyya kuma mai hada kan mutane. Ya burge 'yan Burundi a farko saboda tunanin da yake da shi wajen kirkiro hada kai a kan harkokin noma ta hanyar da 'yan Burundi za su sarrafa abin da suka noma domin kawo karshen noma abu daya na gahawa. Na biyu kuma dangantaka da sauran jiga-jigan 'yan Afirka inda Yarima Louis Rwagasore ya gamu da Patrice Lumumba na Kwango. Sau da yawa ya yi musanyar wasiku da Shugaba Gamel Abdel Nasser na Masar kana da kulla abokantaka da Julius Nyerere. Harkokin noma da Louis Rwagasore ya kirkiro ya rushe amma hakan ya janyo masa shahara, inda ya kafa jam'iyyar "parti de l'Union et du Progrès national” (National Progress and Unity Party) (UPRONA), a shekarar 1958 domin hada kan kasa.

 

Ina matsayin da yake tsakanin mashahuran 'yan Afirka da ke zama gwarzayen samun 'yanci?

A Burundi ya kasance gwarzo da ake girmamawa duk lokacin bikin samun 'yancin kai kana ya zama alama ta hadin kai lokacin da ake shirye-shiryen samun 'yancin Burundi cikin kwanciyar hankali. A wuraren wasanni da makarantu da dakunan karatu ana girmama wannan gwarzo na kasa. Bayan yakin basasa na Burundi, an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2000 a birnin Arusha na Tanzaniya da zummar mutunta "kwarjinin shugabancinsa" ga 'yan Burundi. Ya zama wanda ake girmamawa a duk wani biki na kasa da na samun 'yanci kuma wanda ya taka rawa a hanyar samun 'yancin Burundi - har aka samu 'yancin. Mutuwar da ya yi da wuri ta hana masa duba "hakikanin matsalolin kasa: musamman na tattalin arziki da rabon filaye da hadin kan mutane da ilimi da sauran lamura da za mu samar da mafita ga kanmu." Kamar yadda ya fada lokacin da yake jawabin zama firaminista.

 

Shiri na musamman "Tushen Afirka" aiki ne na hadin gwiwa tsakanin DW da Gidauniyar Gerda Henkel.