1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a boren kin amincewa da Tshisekedi

Yusuf Bala Nayaya
January 10, 2019

Mutane hudu sun halaka a zanga-zangar da ta barke a Kwango biyo bayan bayyana sakamakon zabe da Martin Fayulu ya ki amincewa da shi. Hukumar zaben kasar ta bayyana Felix Tshisekedi a matsayin sabon shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3BLCW
Archivbilder: Bundeswehreinsatz im Kongo 2006
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Zaben da ya kafa tarihi a wannan kasa da ta yi kaurin suna a tashe-tashen hankula  inda wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki a hannun wata ta farar hula. Sakamakon zaben na kasar ta Kwango da aka yi ranar 30 ga watan Disamba ya zo da ba zata inda ake tsammanin Emmanuel Ramazani Shadary da ke samun goyon baya na shugaban kasa Joseph Kabila zai lashe shi ganin yadda yake zama na kusa da shugaban, sai kawai ba tsammani shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Kwango CENI Corneille Nangaa ya baiyana Felix Tshisekedi a matsayin wanda ke da rinjaye a zaben. Lamarin da ya haifar da tsallen murna ga bangaren na adawa bangaren Tshisekedi.

Félix Tshisekedi
Hoto: Reuters/B. Ratner

 Tshisekedi, na jam'iyyar UDPS dan shekaru 55 ya samu kuri'u miliyan bakwai yayin da Shadary ya samu sama da miliyan hudu da Martin Fayulu shi ma da ke zama dan adawa ya samu sama da miliyan shida. A cewar Tshisekedi daga wannan lokaci ba ya daukar kansa da Shugaba Kabila a matsayin abokan adawar juna sai dai abokan gwagwarmaya ta siyasa don samar da sauyi a kasar.

Shadary dai da aka tsammaci shi zai kai labari a zaben ya taya murna ga Tshisekedi sai dai Fayulu wanda ya yi kira ga bangaren Shugabanni a cocin Katolika su bayyana nasu sakamakon bayan da suka tura kimanin masu sa'ido 40,000 da sakamakon ya fara nuna cewa shi ne a gaba don haka ya yi watsi da sakamakon na hukumar CENI da ya ce babu komai ciki sai aringizon kuri'u.

Tuni dai kasashe ke mayar da martani kan zaben na Kwango ciki kuwa har da Faransa wacce ministan harkokin wajenta Jean- Yves Le Drian ya ce duk da an yi zabe lafiya ba haka suka tsammaci sakamakon ba.     

Kongo Abt Donatien N'shole
Hoto: Getty Images/AFP/J.D. Kannah

Ita kuwa kasar Beljiyam ta bakin minisatan harkokin wajenta Didier Reynders nuna shakkunta ta yi kan sakamakon da ta ce za ta nemi tabbaci na sahihancinsa.