1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron da Buhari za su yaki ta'addanci

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 4, 2018

A ci gaba da ziyarar da yake a Najeriya, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Lagos cibiyar kasuwancin kasar, inda ya halarci wajen shagalin bikin tuna wakokin Fela Kuti.

https://p.dw.com/p/30pUp
Nigeria Abuja Emmanuel Macron und Präsident Muhammadu  Buhari
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: DW/U. Musa

Da isarsa birnin na Lagos, Macron ya halarci wani shagalin biki a wajen da ake gudanar da wakokin tunawa da shahararren mawakin nan na Najeriyar da ya yi fice a wakokin afrobeat Fela Kuti. Macron dai ya halarci wannan bikin ne bayan ganawarsa da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari inda suka sha alwashin hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a Afirka ta yamma baki daya.