Macron ya yabi sojojin Faransa a waje
December 23, 2018Talla
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gana da dakarun kasar ta Faransa a kasar Chadi inda ya yaba masu kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin.
Da yake jawabi ga sojoji 1000 a birnin N'Djamena ya ce duk inda Faransa ke yakar 'yan ta'adda kare kanta take domin irisu ne suka kai hari a birnin Strasbourg.
Faransa dai na da dakarun soja 4,500 wadanda ke aiki cikin rundiyar Barkhane masu yakar 'yan ta'adda a Chadi da Mali da Burkina Faso da Mauritaniya da Mali da Nijar.