1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafi yawan sojojin Rasha sun janye daga gabashin Ukraine

Mohammad Nasiru AwalSeptember 10, 2014

A ranar Jumma'a da ta gabata bangarorin da ke rikici da juna a gabashin Ukraine suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a wani taro da suka yi a Minsk.

https://p.dw.com/p/1DA4i
Ukraine Petro Poroschenko in Mariupol
Hoto: Reuters/M. Lazarenko/Ukrainian Presidential Press Service

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya ce Rasha ta janye mafi yawan sojojinta daga gabashin Ukraine. Shugaban ya fada wa wani zaman majalisar ministocinsa a birnin Kiev cewa bayanan hukumomin leken asiri na baya-bayan nan sun nuna cewa kimanin kashi 70 cikin 100 na sojojin Rasha sun koma cikin yankin Rasha. Ya kuma gabatar da wani shiri na musamman ga yankunan Donezk da Luhansk da ke hannun 'yan tawaye magoya bayan Rasha. Ya ce a mako mai zuwa zai gabatar wa majalisar dokoki wani shirin doka bisa manufar samar da matsayi na musamman ga wadannan yankuna. A makon da ya gabata ne Rasha da Ukraine suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta tanadi tsagaita wuta da kuma musayar firsinoni. Har yanzu kuwa bangarorin biyu na girmama shirin tsagaita wutar.