1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita ga rikicin siyasar Masar

November 29, 2012

Masar ta ce akwai yiwuwar ƙuri'ar raba gardama akan tsarin mulki ta warware rkicin da ƙasar ke fama dashi.

https://p.dw.com/p/16ssJ
The Islamist-dominated panel vote on a final draft of a new Egyptian constitution in Cairo, Egypt, Thursday, Nov. 29, 2012. The assembly, overwhelmingly made up of allies of President Mohammed Morsi, abruptly moved up the vote which hadn't been expected to take place for another two months in order to pass the draft before Egypt's Supreme Constitution Court rules on Sunday on whether to dissolve the panel. (Foto:Mohammed Asad/AP/dapd)
Hoto: AP

Shugaba Mohammad Mursi na Masar, wanda ƙasarsa ta faɗa cikin ruɗanin siyasa bayan daya ɗauki matakin fa'ɗaɗa ikon daya ke dashi, ya bayyana cewar jefa ƙuri'ar raba gardama akan tsarin mulkin ƙasar ka iya kawo ƙarshen rikicin. Shugaban ya furta hakanne a dai dai lokacin da majalisar da ke rubuta sabon tsarin mulkin ƙasar ta fara jefa ƙuri'ar ƙarshe na amince da daftarin tsarin mulkin. Dama dai shugaba Mursi ya ɓullo da wata sabuwar doka ce, wadda ta haramtawa kotuna ƙalubalantar matakan da zai ɗauka- har na tsawon watanni biyu, abinda kuma ya janyo mummunar suka daga 'yan adawa da kuma ɓangaren shari'ar ƙasar, yayin da jam'iyyarsa ta Muslim Brotherhood kuma ke ci gaba da nuna masa goyon baya. Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu daga cikin 'yan ƙasar ta Masar ke ci gaba da yin zaman dirshen a dandalin Tahrir don neman yayi watsi da matakin daya ɗauka.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou