Magance matsala ta hanyar kaifafa tunani da zane

Cibiyar kaifafa basira ta hanyar zane ta Hasso Plattner da ke Jamus ta kaddamar da makaranta ta farko a Afirka. A birnin Cape Town makarantar na koyar da dalibai hanyoyin warware matsaloli daban-daban.