1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata na ci gaba da zuwa birnin Makka

Salissou BoukariSeptember 18, 2015

Fiye da mutane miliyan biyu ne mahajjata suka fara hallara a birnin Makka na Saudiyya domin gudanar da ayyukan su na hajjin bana duk da batun tsaro da ke daukan hankali a Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1GYjl
Hoto: Tohlala/AFP/Getty Images

Duk da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin na Gabas ta tTsakiya, mahajjatan na bana na cike da niya da kuma nutsuwa, inda suke fitowa daga sassa daban-daban na duniya domin gudanar da ayyukansu wanda a hakumance ke fara wa daga ranar Talata mai zuwa. Da yake magana da 'yan jaridu kan batun matsalar tsaro da wasu ke ikirari, Amine Al-Rahmane, wani mahajjaci dan kasar Bangladesh cewa ya yi, "ku duba dubban wadannan mutane, kuna tsammani akwai tsoro a zukatansu", yace "sai dai sabanin haka".

A ranar Alhamis ma dai dubunnan mahajjata ne 'yan yankin kasashen Asiya aka kwashe daga masaukinsu sakamakon wata gobara da ta tashi cikin dare a Hotel din da suke, yayin da tun farko kuma wani mumunan hadari ya haddasa rasuwar mutane fiye da 100 sakamakon fadowar da wani injin daukan kayyakin ginene ya yi.