1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahajjata na gudanar da tsayuwar Arfa

Ahmed SalisuOctober 3, 2014

Kimanin Musulmi milyan biyu ne suke gudanar da aikin hajjin bana a Saudi Arabia kuma a wannan Juma'ar ce mahajjata ke tsaiwar Arfa yanzu haka.

https://p.dw.com/p/1DPVk
Muslime beten am Berg Arafat 03.10.2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Al-Shaikh

Tun a jiya ne dai alhazan suka isa Muna kuma da sanyin safiyar Juma'ar nan ce suka dunguma zuwa dutsen Arfa don gudanar da aiyyukansu na ibada.

Hukumomin Saudiyya dai sun ce sun gudanar shirye-shirye a bana don kawar da duk wasu matsaloli da mahajjatan ka iya cin karo da su yayin da aikin hajjin na bana ya kai kololuwarsa.

Masu aiko da rahotanni dai na cewar komai na gudana lami lafiya ba tare da an fuskanci wani kalubale babba ba.