1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun kai farmaki a Mozambik

May 10, 2024

Sabon fada ya barke tsakanin dakarun sojin Mozambik da kuma 'yan bindiga a yankin Macomia da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4fjCk
Mahara sun kai farmaki a Mozambik
Mahara sun kai farmaki a MozambikHoto: Marc Hoogsteyns/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Mozambik, Filipe Nyusi ya ce dakarun kasar na fafatawa a fagen daga da 'yan bindigar da suka kai hari birnin Macomia, lamarin da ya haifar da rincabewar rikici a arewacin kasar. Shugaba Nyusi ya ce dakarun kasar sun samu damar fafattakar 'yan bindigar da suka yi yunkurin shiga birnin a ranar Juma'ar bayan kwashe tsawon mintuna 45 a musayar wuta. Sai dai kuma a cewarsa, mayakan sun sake sabon shiri tare da komawa yankin.

Karin bayani: Mozambik: Masu jihadi na dada kai hare-hare

Harin na zama mafi muni a jerin hare-haren da aka kai wa yankin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas a shekarar 2024. Kafafen yada labarai na cikin gida, sun ruwaito cewa daruruwan mahara na zafafa kai farmaki a daidai lokacin da babban kamfanin makamashi na kasar Faransa ke shirin zuba jarin dala biliyan 20 a shirin samar da iskar gas a yankin.

Tun dai a shekarar 2017 kasar Mozambik ke fama da matsalolin kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu biyar yayin da wasu dubbai suka rasa matsugannsu.