1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Brexit: May ta sha kaye a majalisar dokoki

Abdullahi Tanko Bala
March 13, 2019

'Yan majalisar dokokin Birtaniya a karo na biyu sun sake yin fatali da kudirin yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta cimma da Kungiyar Tarayyar Turai EU.

https://p.dw.com/p/3Euih
Großbritanien | Theresa May spricht im Unterhaus | Brexit | London
Hoto: Reuters/UK Parliament/J. Taylor

A kuri'ar da 'yan majalisar suka kada a ranar Talata, yan majali 391 sun ki amincewa da yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta gabatar yayin da 'yan majalisa 242 suka ce sun yarda.

Firaministar ta ce ta ji matukar takaici da matakin da 'yan majalisar suka dauka.

Sai dai da yake jawabi shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn yace ya kamata Theresa May ta sauya tunani kan kudirinta na neman ficewarBirtaniya daga kungiyar tarayyar Turai ba tare da cimma yarjejeniya mai ma'ana ba. 

Yace gwamnati ta kuma shan kaye da gagarumin rinjaye. A yanzu wajibi ne su amince cewa shawarar su da yarjejeniyar da Firaminista ta gabatar basu sami amincewar wannan majalisar ba.

Firaminista Theresa May dai ta ce ta yi imani hanya mafi dacewa ita ce rabuwa cikin masalaha da karimci tsakanin Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai.