1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kai agaji a Iraƙi

August 19, 2014

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta bayyana cewar za ta ƙaddamar da ayyukan kai kayan agaji ga mutane sama dubu 500 da yaƙi ya ɗaiɗaita a arewacin Iraƙi.

https://p.dw.com/p/1Cwwb
Irakische Fllüchtlinge in Erbil, Nordirak
Hoto: Karim Sahib/AFP/Getty Images

Dubban darurruwan mutane ne dai suka ƙaurace wa matsugunansu tun bayan da mayaƙan IS suka mamaye arewaci da yammacin wannan ƙasa a watan Yuni inda su ke barazanar raba ƙasar.

Wani mai magana da yawun sashin kula da 'yan gudun hijirar na MDD Adrian Edwards, ya ce aikin rarraba kayan agajin na kwanaki huɗu, sun haɗa da tantina da sauran abin masarufi.

Kana ya ƙara da cewar Za'a fara aiki ne a gobe Larba , kuma zai dangana da yankin Arbil daga Aqaba a Jordan, har ila yau wasu kayan za su fito daga Dubai ta hanyar amfani da jirgin ruwa da zai ratsa ta Iran nan da kwanaki 10.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita : Abdourahamane Hassane