1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta ja kunnen Turkiya

Salissou Boukari
May 1, 2017

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakin dan Adam Zeid Ra'ad Al Hussein ya yi kira ga kasar Turkiya da ta bi hanyoyin da suka dace dangane da kame-kamen da take yi ga mutanen da take zargi.

https://p.dw.com/p/2cBXj
USA UN-Menschenrechtsrat Said Raad al-Hussein
Zeid Ra'ad Al Hussein shugaban hukumar kare hakin bil-Adama ta Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Imago/Zuma Press

Yayin wani taron manema Labarai ne dai a birnin Geneva, mai kula da kare hakin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da korar ma'aikata kusan dubu 4 da hukumomin na Turkiya suka yi daga bakin aiki cikin su akwai jami'an ma'aikatar shari'ar kasar dubu 1 guda sannan wasu dubu a fannin jami'an tsaro inda yake cewa "rabin 'yan jaridar da aka aike da su gidan kason, an daure su ne a Turkiya. Wannan abu na damunmu domin kuwa aikin jarida ba laifi ba ne a kasar Turkiya. Wannan matsala dai aba ce da muke ganin ya kamata hukumomi su sanya ido sosai a kanta.''

Tun dai daga yunkurin juyin mulki da aka yi na ranar 15 ga watan Yuli na 2016 kawo yanzu an kama mutane dubu 47 a kasar da ake zargi suna da alaka da sheihin Malamin nan dan kasar ta Turkiya  Fethullah Gulen da ke gudun hijira a Amirka.