1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya za ta tura runduna zuwa Mali

April 26, 2013

A wani zama da ya yi a birnin New York komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tsai da shawarar tura sojoji da yan sanda dubu 12 zuwa kasar Mali

https://p.dw.com/p/18Nbv
Hoto: picture-alliance/dpa

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) zai yi haka ne kafin tura dakarun Afirka zuwa wannan kasa da za a yi daga watan Yuli. Rundunar soji da 'yan sandan da MDD ta ya yi wa suna "Minusma"  za ta taimaka wa gwamnatin Mali a yakin da ta ke yi da 'yan kishin islama da 'yan aware da ke arewacin kasar domin maido da kwanciyar hankali. 

A dai halin yanzu sojoji Faransa 4000 ne ke taimaka  wa dakarun kasar ta Mali da na kasashe makwabta da ke yaki da 'yan tawayen. Tun wasu watannin kenan da Faransa da kasashen Afirka ke yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta karbi wannan aiki, ta kuma samar da kudin tallafa wa dakarun Afirka da  za a tura zuwa kasar ta Mali.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar