1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar rikon kwaryar Haiti ta kafa shugabancin karba-karba

May 11, 2024

Sabuwar majalisar rikon kwaryar Haiti ta kafa shugabancin karba-karba a cikin wani kudiri da ta dauka bayan tuntubar juna da nufin kawo karshen rashin jituwa da ke neman durkusar da wannan hukuma.

https://p.dw.com/p/4fjci
Majalisar rikon kwaryar Haiti ta kafa shugabancin karba-karba
Majalisar rikon kwaryar Haiti ta kafa shugabancin karba-karbaHoto: Ramon Espinosa/dpa/picture alliance

Wannan kudiri da aka cimma ta hanyar yarjejeniya na zuwa ne bayan baraka da ta taso a cikin majalisar bayan nadin Edgard Leblanc Fils a matsayin shugaba a karshen watan Afrilun da ya gabata lamarin da ya ke neman dabaibaye gudanarwar hukumar.

Karin bayani: Jagororin siyasar Haiti sun amince da kafa gwamnatin rikon kwarya

Sabuwar yarjejeniyar ta shata cewa mista Leblanc Fils zai ci gaba da zama a matsayin shugaban hukumar da aka dora wa alhakin dawo da Haiti kan tafarkin dimokuradiyya har zuwa ranar bakwai ga watan Oktoba na wannan shekara.

Sannan kuma Smith Augustin zai maye gurbinsa daga wannan lokaci zuwa bakwai ga watan Maris na 2025, sai kuma Leslie Voltaire ya karba zuwa bakwai ga watan Ogustan 2025 kafin daga karshe Louis Gérald Gilles shima ya karba zuwa bakwai ga watan Fabarairu na 2026.

kazalika Majalisar rikon kwaryar ta Haiti ta kuma amince da wasu sabbin dokoki ciki har da dokar nadin Firaiminista da gwamnati.