1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilan Amirka ta yi fatali da shawarar janye dakarun kasar daga Iraqi

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKX

Majalisar wakilan Amirka ta yi watsi da wani kuduri da ya nuna bukatar janye dakarun kasar daga Iraqi nan take, bayan wata zazzafar muhawwara akan rarrabuwar kawuna dangane da yakin Iraqi. Tare da gagarumin rinjaye wakilan majalisar sun ki amincewa da kudurin wanda wakilan jam´iyar Republican suka gabatar, wanda ya soke wata shawara da dan jam´iyar Democrat John Murtha ya gabatar. A ranar alhamis da ta gabata dan majalisar ya gabatar da shawarar janye dakarun Amirka dubu 138 daga Iraqi amma a maye gurbinsu da wata rundunar kundunbala wadda za´a girke ta a wata kasa ta yankin Golf. Murtha ya nunar da cewa ba za´a ci Iraqi da yaki da karfin soji ba. Ya ce ta hanyar lumana ce kadai za´a warware wannan rikici.