1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makaho mai cibiyar koyar da masu idanu sana'a

Ado Abdullahi Hazzad/GATJanuary 20, 2016

A Bauchi, wani makaho mai suna Abubakar Abdullahi, ya tashi tsaye wajen taimaka wa al'umma ta hanyar bude wata cibiya domin koyar wa masu ido matasa irin fasahar da Allah ya yi masa ciki har da yin man shafawa

https://p.dw.com/p/1Hh5Z
DW AOM - Bauchi Blind
Hoto: DW/A.A. Hazzad

A Bauchi, wani makaho mai suna Abubakar Abdullahi wanda ke cikin kuriciyarsa a lokacin da cutar makanta ta sameshi, ya tashi tsaye wajen taimaka wa al'umma ta hanyar bude wata cibiya domin koyar wa masu ido matasa maza da mata irin fasahar da Allah ya yi masa ciki har da yin man shafawa da na wanke gashi,

Abubakar Abdullahi, wanda ya ce ya makance ne a dare daya a yayin da yake karatu a Jami'ar Bayero da ke Kano yana shekara ta ukku, amma ya ce wannan nakasa da ta same shi ba, ba za ta hana shi rayuwa mai kyau ba, shi ya sa ya ce ya shiga wata makarantar nakasassu domin koyon sana'a da za ta sa ya cimma burinsa domin kuwa ya ce shi ba zai yi bara ba saboda wannan makanta da ta same shi.

Ya ce ya bude wata cibiya da yake koyawa masu ido sana'a da za su dogara da kansu kamar yin man shafawa, man wanke gashi wato shampoo turaraen kanshi na sawa a gida dama sake-sake kayan ado

DW AOM - Bauchi Blind
Hoto: DW/A.A. Hazzad

da dai sauransu, ya ce ya yaye dalibai fiye da dubu kawo yanzu kuma a yanzu akwai kusan dalibai 400 da yake koya musu sana'o'in.

Ya ce burinsa a yanzu shi ne ya ga cewa ya canja tunanin al'umma wadanda ke ganin cewa duk wanda ya samu nakasa ko wata larura shikenan ba shi da wani amfani shi ya sa yake son ya ga an kauda wannan ra'ayin.