1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makokin 'yan yawon buɗe daga Hong Kong

August 26, 2010

Hong Kong ta yi zaman makokin 'ya'yanta 8 da suka mutu a Filipins

https://p.dw.com/p/Owhh
Dakarun tsaron Filipins a lokacin da suke ƙoƙarin ƙwato waɗanda aka yi garkuwa da su.Hoto: AP

A Hong Kong, an yi zaman makokin wasu 'yan wannan jiha su 8 da suka gamu da ajalinsu a ƙasar Filipins bayan da wani tsohon ɗan sanda ya yi garkuwar da su bisa buƙatar mai da shi bakin aikinshi. Kimamin mutane ɗari biyar ne dai suka halarci wannan zaman da gwamnan wannan yanki, Donald Tsang ya jagoranta a dandalin Bauhinia. Sai da aka yi kawaici na minti uku tare da sassauta tutoci domin tunawa da marigayan da suka gamu da ajalinsu da yammacin Litinin da ta gabata. 'Yan yawon buɗe ido guda 8 ne suka mutu wasu kuma su 7 ne suka samu raunuka bayan da Ronaldo Del Rosario tsohon ɗan sandan ƙasar ta Philippines ya shafe awa goma yana garkuwa da su bisa buƙatar mai da shi bakin aikinshi. Daga cikin waɗanda suka halarci zaman makokin har da biyar da suka tsira da rayukansu da kuma jami'an gwamnati. Da yammacin jiya Laraba ne aka ɗauki gawawwakin zuwa Hong Kong.

Mwallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu