1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Mosul bayan fatattakar IS

Ahmed Salisu
July 11, 2017

Bayan karbe ikon birnin Mosul daga kungiyar IS a karshen mako, yanzu hankulan al'ummar birnin da ma kasar ya fara karkata ne kan makomar birnin mai tarihi da ya jima a hannun mayakan na IS da ke rajin kafa daular Islama.

https://p.dw.com/p/2gKWh
Irak, Der irakische Premierminister Haider al-Abadi hält eine irakische Flagge, als er den Sieg über den islamischen Staat in Mosul verkündet
Tayin murna ga sojojin Iraki da suka yi nasarar kwato MosulHoto: Reuters

Duk da cewar rundunar sojin Iraki ta samu nasara wajen karbe iko da birnin Mosul wanda a baya ya kasance babbar tunga ta mayakan kungiyar IS, da dama na fargaba kan irin yadda lamura za su kasance a wannan birni musamman ma batun rikon madafun iko duba da irin kabilu da mabiya tafarki na addinin Islama iri-iri da a baya suke cikin birnin. Masana harkokin tsaro na ganin akwai alamar jan zare tsakanin Kurdawa da ke birnin wanda ke samun goyon bayan mahukuntan Kurdistan da kuma mabiya tafarkin Shi'a da ke samun tallafin kasar Iran, sai kuma 'yan Sunni wadanda su ma suka rigaya suka girku a wannan birni kuma suke son ganin sun samu sukunin jagorantarsa kamar dai yadda 'yan Shi'a da Kurdawa ke son samu.

Die Proteste in Bahrain gegen das Formel 1rennen breiten sich aus
'Yan Shi'a a IrakiHoto: DW/K.Leigh

Rayk Hähnlein mai sharhi kan lamuran da suka danganci kasar ta Iraki, ya ce daya daga cikin matsalolin da yanzu haka Iraki za ta yi fama da su ita ce wanda zai rike madafun iko a birnin Mosul. Abin da ke a bayyane shi ne ba zai yiwu Kurdawa ko kuma mabiya tafarkin Shi'a su mulki gari na wani tsawon lokaci ba to amma kuma yadda za a yi wajen warware wannan matsala ta wannan birni wanda galibinsa labarawa ke zaune ciki abu ne da ke da wuyar fadi.

Bisa ga irin abin da ya wakana lokacin da ake gumurzu wajen karbe iko da birnin na Mosul dai Kurdawa sun taka rawa wajen koran 'yan IS kuma suna ganin wannan nasara da aka samu wata dama ce ta cimma burin da suka sanya a gaba musamman ma dai da ya ke suna dab da yin kuri'ar raba gardama ta samun 'yancin na yankinsu wanda hakan zai wakana cikin watannin da ke tafe kamar dai yadda Renad Mansour na cibiyar Chatam House da ke Birtaniya ya shaida.

Ya ce ''A halin da ake ciki suna kokari ne na maida yankin cikin kasarsu da suke ayyana 'yancinta kuma baya ga Mosul ma za su yi kokari wajen sanya yankin Kirkuk idan aka yin kuri'ar raba gardama cikin watan Satumba da ke tafe''

Mayakan Kurdawa
Mayakan KurdawaHoto: Reuters/G. Tomasevic

To yayin da Kurdawan ke wannan fafutuka, su ma 'yan Shi'a da suka bada tasu gudunmawa a wannan yaki na ganin lokaci ya yi da za a saka musu da alheri kan irin bajintar da dubban mayakansu suka yi kuma suna son ganin an yi hakan ne ta hanyar basu dama wajen kankane madafun iko a birnin na Mosul. Da ma dai masana da dama sun sha bayyana cewar kokarin kawar da 'yan kungiyar IS daga Mosul ne ya sanya lafawar fafutuka ta karbar iko da wannan birnin kuma ma dai haka abin yake a birnin Raqqa inda nan ma ake son ganin an kawar da mayakan IS daga cikin.

Abin jira a gani shi ne irin alkiblar da wannan cece-kuce na neman shugabanci zai fuskanta da kuma yadda za a wanye idan kura ta lafa.