1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar 'yan gudun hijira daga Libiya a gida Najeriya

January 12, 2018

Wani dan gudun hijrar dan asalin jihar Edo da aka dawo da shi daga Libiya ya ce wasu 'yan Najeriya sun siyar da shi a kan Naira 150,000 a Libiya kafin daga bisani ya samu kansa bayan da mahaifiyarsa ta biya diyya.

https://p.dw.com/p/2qlor
Nigera Flüchtlingsrückführung aus Libyen
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Jirage na ci gaba da kawo 'yan Najeriya da ke jibge a kasar Libiya bayan da aka gano kasuwar cinikin bayi da ta harzuka mahukuntan kasashe da al'ummarsu suka dauki harami na zuwa Turai ta hanyar ratsa kasar ta Libiya.

Gwamnatoci dai na jihohi sun shirya karbar al'ummarsu da a ke dawowa dasu ta yadda ake shiri na sama masu makoma a kasarsu ta haihuwa. A jihar Edo da al'ummarta ta fi yawa cikin 'yan hijirar ta Najeriya ta ce ta shirya basu Naira dubu 20 a duk wata tsawon watanni uku kafin a tantance sana'ar da za su yi  a nan gaba.

Nigeria Flüchtlinge kehren nach Lagos zurück
Mata da yara sun ga ta kansu a LibiyaHoto: picture alliance/dpa/AP Photo/S. Alamba

Wani dan gudun hijrar dan asalin Edo Victor Nelson da aka dawo da shi daga Libiya ya ce wasu 'yan Najeriya sun siyar da shi a kan Naira 150,000 a Libiya kafin daga bisani ya samu kansa bayan da mahifiyarsa ta biya diyya.

Wasu 'yan Najeriya dai na da mabanbantan ra'ayoyi kan halin da 'yan gudun hijirar ke ciki, wasu na cewa ya kamata gwamnati ta yi masu wani abu da za su dogara da kansu yayin da wasu ke ganin cewa gwamnati ta gama yi masu komai ganin yadda ta 'yantosu daga kokari na bautar da su a kasar ta Libiya. Wasu ma na ganin cewa ai sun san hanyoyi da suka bi suka samu makudan kudade kafin kama hanyar zuwa Turai don haka su sake bi su rufawa kansu asiri a gida.

A kasashen Afirka da dama dai har kawo yanzu ana ci gaba da tattauna wannan batu na kokarin maido da cinikin bayi ta hanyar siyar da matasa da ke da buri na zuwa Turai ta barauniyar hanya a Libiya.