1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Malawi ta rage darajar kudin kasar

Abdul-raheem Hassan
May 27, 2022

A wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar da ke fama da rauni da kuma dakile hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin Malawi ta rage darajar kudin kasar da kashi 25 cikin 100.

https://p.dw.com/p/4BvPx
Afrika Symbolbild Zambia Währung Kwacha
Hoto: Imaginechina-Tuchong/imago images

Sanarwar ta fito ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta kaddamar da tattaunawa da asusun ba da lamuni na duniya IMF kan shirin farfado da tattalin arzikinta.

Babban bankin ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa rage darajar kudin mafi girma cikin shekaru goma, zai fara aiki daga yau Juma'a. Lokaci na karshe da Malawi ta samu gagarumin faduwar darajar kudinta, shi ne a shekarar 2012, inda aka rage darajar kudin kasar mai suna kwacha da kashi 33 cikin 100.

Babban bankin kasar ya ce annobar coronavirus ta haifar da raguwar kudaden da ake samu daga kasashen waje, kuma kudaden shigo da kayayyaki sun karu da hauhawar farashin kayayyaki saboda yakin Ukraine. Har ila yau, bankin ya ba da misali da tarzomar da ta haifar da barnar da guguwar ruwa guda biyu da ta afkawa kasar a farkon shekarar 2022.

"Rashin daidaiton bukatu ya bayyana a kasuwar canji ta cikin gida ta hanyoyi da dama, ciki har da karancin wadatar kudaden waje da raguwar kudaden ajiyar waje na hukuma,” in ji bankin.

Ministan kudi a Malawi, Sosten Gwengwe ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa gwamnati ta shirya shirin rage darajar "dan lokaci kadan”. "Dole ne mu yi wannan," in ji shi. YA kara da cewa "Babban bankin yana kokawa saboda kimar kudin kasar wato Kwacha".

Mr Gwengwe ya ce aikin na IMF zai ci gaba da wasu makonni uku zuwa hudu. Karuwar farashi a kasar Malawi a watan Afrilu na shekarar 2022 ya kai kashi 15.7 bisa 100, sakamakon tashin farashin abinci da sauran kayayyaki.