1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Harin bam ya kashe mutane 47

Zainab Mohammed Abubakar
January 18, 2017

Harin da ya auku a Gao, ya ritsa da sansanin sojojin tsoffin mayakan sa kai na gwamnati da masu tsananin kishin addini, da suka kwace madafan ikon yankin arewacin Mali a farkon shekara ta 2012.

https://p.dw.com/p/2Vzmo
Mali Anschlag in Gao
Hoto: Getty Images/AFP

Harin kunar bakin wake da aka kai da wata mota ya yi sanadiyyar rayukan mutane 47 a sansanin soji a garin Gao da ke yankin arewacin kasar Mali.

Sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun sojin Mountaga Tall na nuni da cewar, daga cikin wadanda suka mutun har da 'yan kunar bakin waken guda biyar, a yayin da wasu mutanen 115 suka jikkata, 30 na cikin mawuyacin hali.

A cewar  Abdedoula El Kader Toure na kungiyar sa kai ta Gao, wata mota ce makare da wasu abubuwan fashewa masu nasaba da bam, ta tarwatse a daidai lokacin da sojojin suke taro.

An yiwa motar fentin launin soji, wanda ya bata saukin shiga cikin sansanin ba tare da wata matsala ba.