1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali na daukar mataki kan kasashen duniya

Abdourahamane Hassane
January 21, 2022

Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta haramta wa wani jirgin soji na Jamus ketta sararrin samaniyarta a kan hanyarsa ta zuwa Nijar. Jamus dai na adawa da dorewar mulki soji a Mali.

https://p.dw.com/p/45u3n
L-410 Militärflugzeug
Hoto: Vitaliy Belousov/picture alliance/dpa/Sputnik

Jirgin na rundunar sojojin Jamus wanda ke dauke da sojoji guda 80 da ya taso daga birnin Berlin, ya canza hanya ya sauka a tsibirin Kanari na Espain daga can ya isa Nijar. Jamus na da yawan sojoji sama da dubu daya da ke da sansani a Nijar da ke aikin tabbatar da tsaro a Mali,  wadanda ke aiki tare a rundunar Takuba ta kasashen Turai da kuma Barkahn.Hukumomin Mali sun rufe kan iyakokinsu bayan da kungiyar Ecowas ta saka wa kasar takunkumi tare da rufe kan iyakokinsu saboda kin bayyana jadawalin sabon zabe da hukumomin Malin suka yi.