1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali tana cikin wani hali na tsaka-mai-wuya

February 1, 2013

Jaridun na Jamus kusan gaba dayansu sun maida hankali ne a wannan karo game da nahiyar Afirka kan kasar Mali da halin da ake ciki na yaki a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/17WRs
Hoto: dapd

Jaridar Die Zeit ta duba sabuwar matsalar da ta kunno kai a arewacin kasar, inda sojojin gwamnati ake zarginsu da kisan abokan adawa da duk wadanda suka zargesu da hannu, ko taimakawa yan tawaye da kungiyoyi na musulmi, a wani mataki na daukar fansa. Jaridar ta ambaci wani ma'aikacin taimakon raya kasa na Jamus a arewacin Malin yana cewar kusan kowa a kauyukan yankin zaune yake cikin hali na tsoro, saboda ramuwar gaiya ta hanyoyi masu tsanani da sojojin na gwamnati suke yi a can. Yayin da sojojin Faransa a tsawon kwanaki 17 da suka yi suna yaki a kasar ta Mali, sun karbe garuruwa da dama, amma munanan labarai suna fitowa daga wadannan garuruwa dake cewar sojojin Mali suna daukar fansa kan duk wanda suka ci karo dashi kuma suka ga alamun yana da wata dangantaka da yan tawayen.

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba kokarin da Faransa da gwamnatin Mali suke yi ne na jan hankalin Buzaye yan tawaye a arewacin Mali domin shiga tattaunawar neman zaman lafiya. Tun kafin baiyanar a wannan bukata da sojojin Faransa suka sanar da cewar sun mamaye garin Kidal, mai matukar muhimmanci, dake da nisan kilomita 1500 daga arewa maso gabashin birnin Bamako. Gwamnatin Mali tace a shirye take ta tattauna da Buzayen yan tawaye, amma ba zata zauna kan teburin shawarwari daya da kungiyoyi masu kishin Islama ba. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace ganin cewar Faransa ta sake kwato mafi yawan garuruwan da kungioyoyin musulmi ko na yan tawaye suka mamaye, yanzu lokaci yayi da Faransa zata maida hankalinta ga neman sulhu na siyasa tsakanin dukkanin yan kasar ta Mali.

A farkon wannan makone aka gudanar da taron kasa da kasa da kungiyar hade kan Afirka wato AU ta shirya a Addis Ababa na Habasha, inda wakilai suka yi nazarin taimakon kudi ga kasar Mali, a matakan sake gina kasar bayan yaki. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta maida hankalinta ga wannan taro, inda tace a lokacinsa, kasashe sun yi alkawarin tarawa Malin taimakon kudi Euro miliyan 338, inda gwamnatin Jamus tayi alkawarin bayar da Euro miliyan 14.9 na wannan adadi, yayin da kungiyar hadinkan Turai zata bayar da gudummuwar Euro miliyan 50. Wannan kudi da zai kasance a wani asusu da majalisar dinkin duniya zata kula dashi, rundunar sojan Mali musamman zata ci gajiyarsa. Bayan kudi, kasashe da dama, inji jaridar sun yi alkawarin taimako a fannoni dabam dabam, akamar misalin Ingila da tace zata bada jami'ai 240 da zasu horad da sojojin Mali, Jamus kuma tace zata kara gudummuwarta ga aiyukan rundunar kasashen ECOWAS dake Mali.

Mali Geberkonferenz in Addis Abeba 29.01.2013
Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius a taron nemarwa Mali taimakoHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

A karshe, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace yakin Mali, koda kasashen yamma sun sami nasarar kawo karshen sa, yana iya zama kamar dai an kashe macijine amma ba'a sare kansa ba. Jaridar ta ambaci wani sharhi cikin wata jaridar ta Holland, mai suna Volkskrant dake cewar abin fata shine, kasashen yamma ba zasu maida hankalinsu kawai a kokarin warware rikicin na Mali ta amfani da karfin soja bane. Halin da Malin take ciki, ya sami asalinsa ne daga zaman gaba dake tsakanin al'ummar bakar fata na Mali da Tuareg, wato Buzaye masu asalin Larabawa a daya hannun. Yanzukuwa akwai alamun cewar bakar fatan kasar da suka dade karkashin danniyar Buzaye, zasu yi amfani da goyon bayan dra suke samu daga sojojin Faransa, domin daukar Faransa kan wadanda suka danne su da duk wadanda suke zaton suna hada kai dasu. Bayan taimakon soja, kamata yayi Faransa ta matsa lamba ga masu mulki a yanzu su nemi sulhu tsakanin dukkanin kabilu da jinsunan kasar ta Mali.

Mali Moschee Zerstörung
Daya daga masallatan da yan tawaye suka lalata a TimbuktuHoto: Reuters