1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Zazzabin cizon sauro a Najeriya

Zulaiha Abubakar AA
October 9, 2018

Zazzabin cizon sauro cuta ce da ta mamaye ko ina a Najeriya, inda yawaitar kyankyasa, yasa saurayen suka karu har suke ta addabar mutane, har da rana tsaka.

https://p.dw.com/p/364Fl

Lamarin da ya zamo jiki ga mutane, inda da zazar anji jiki babu dadi sai a ta hadiyar maganin zazzabin cizon sauraro ba tare da ziyartar Likita ba. Wannan cuta kusan ta zamewa mutane jiki a Najeriya, inda za a tarar da a kalla mutum biyu cikin ko wane gida suna fama da cutar, da zarar kuwa aka ce dare ya yi, sai a ta tururuwar zuwa sayen maganin sauro na hayaki iri-iri, domin turara ko ina, dan korarsu, wasu kuma su bude gidan sauronsu da ake kira ''Mosquito Net'' a turance. Shin ita kuwa, wace irin cuta ce wannan da ta addabi mutane? Ku saurari shirin domin jin karin bayani.

Fiebermuecke, Stechmuecke, Anopheles spec., malaria mosquitoe
Hoto: picture alliance/dpa/blickwinkel/Hecker/Sauer