1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manufar ziyarar Kerry a Afirka

May 2, 2014

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya fara ziyarar aiki ta kwanaki shida cikin kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/1BsoD
Hoto: Reuters

A matakin farko na ziyarar Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yada zango a kasar Habasha (Ethiopia) inda ya gana da ministocin kasashen ketere daga Habasha, da Kenya da kuma Uganda, a birnin Addis Ababa na kasar ta Habasha da ke zama helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka.

Kwanaki kafin ziyarar 'yan sandan Habasha sun garmake mutane shida masu rubuce-rubuce a kafar zamani ta Internet, da 'yan jaridu uku. Kasar Amirka tana kan gaba wajen saka matsin lamba wa gwamnatocin nahiyar Afirka na ganin sakin mara ga 'yan jaridu. Tuni mai magana da yawun Kerry ya nemi gwamnatin Habasha ta saki mutanen.

Masharhanta na ganin mahimmancin kasar ta Habasha ya janyo wannan ziyara, kamar yadda Alex Vines na cibiyar harkokin Afirka da ke birnin London ke fadi:

Demonstration der Blue Party in Addis Abeba, Äthiopien
Hoto: DW

"Habasha ta kasance kasa mai mahimmanci wajen hulda da Amirka, musamman kan yakar ayyukan ta'adanci a yankin gabashin Afirka. Suna da kekkyawar hulda na tsawon lokaci. Amirka ta zuba jari mai yawa kan harkokin ci-gaban kasashe, Sannan kuma da gina mutane da hukumomi a Habasha."

Amirka tana amfani da Habasha wajen lura da abin da ke faruwa a kasashen Somaliya da Sudan ta Kudu. Rikicin da ke faruwa a Sudan ta Kudu na cikin lamarun da Kerry zai tattauna yayin da ya kai ziyara zuwa kasar. Amirka ta taka mahimmiyar ruwa wajen zaben raba gardama na shekara ta 2011, abin da ya janyo Sudan ta Kudu ta samu 'yanci daga Sudan.

A ganin Barack Muluku da ke lura da abubuwa da suke faruwa dan kasar Kenya, ziyarar Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry a wasu kasashen Afirka na da nasaba da tattalin arziki bisa yadda kasashen China da Brazil ke kara kutsawa cikin nahiyar na rage kaifin Amirka.

"Karfin kasashen Yamma da Amirka na raguwa a nahiyar Afirka."

Kasashen Sudan ta Kudu da Angola da Kerry zai kai ziyara na cikin kasashe masu arzikin man fetur. Alex Vines na cibiyar harkokin Afirka da ke birnin London ya ce babu makawa yadda Amirka za ta bunkasa harkokin kasuwanci na cikin muradun kasar:

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

"Haka, wani bangare na ziyarar Kerry a fayyace yake kan kasuwanci. Amma ziyara zuwa Angola da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango zai mayar da hankali kan maganar gabashin Kwango da yadda za a warware rikici. John Kerry, na sani, yayin ziyara zuwa Angola zai yi godiya ta musamman ga Shugaba Jose Edouardo dos Santos saboda a matsayinsa na shugaban kungiyar kasashen tafkin yankin, Angola ta taimaka wajen samar da hanyoyin warware rikicin gabashin Kwango."

Sai dai ana saran gabatar da tambayoyi masu mahimmanci daga dukkanin bangarorin yayin ziyarar ta kwanaki shida da Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ke yi cikin nahiyar ta Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal