1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan hafsoshin soja sun yi taro a Ndjamena

Salissou BoukariAugust 23, 2015

A wani mataki na kammala tsarin ayyukan rundunar hadin gwiwa ta MNJTF da za ta yaki Boko Haram, manyan hafsoshin sojan kasashen biyar sun yi taronsu a birnin Ndjamena na kasar Chadi.

https://p.dw.com/p/1GK7z
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

A ranar Asabar ce manyan hafsoshin sojan kasashe biyar da za su yaki 'yan kungiyar Boko Haram suka kammala tsare-tsarensu na karshe a kokarin da ake na kawo karshen 'yan bindigar da suka addabi kasashen yankin tafkin Chadi. A cewar janar Brahim Seid babban hafsan hafsoshin kasar Chadi, lokaci ya yi na fara aiki, kuma wannan runduna ta hadin gwiwa za ta dauki duk matakan da suka dace domin karbo duk wani yanki daga hannun 'yan ta'adda tare da kawo karshensu baki daya.

Shi kuma wani hafsan soja da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce a cikin wannan zama, kasashen biyar sun tsaida yadda kowa zai bayar da nashi dakaru wadanda ga jumulla za su tashi 8,700 da suka hada da sojoji, jandarmomi da kuma 'yan sanda. Shugabannin sojojin sun tsaida manyan cibiyoyi guda uku na jagorancin rundunar, da suka hada da ta garin Baga Kawa, da ke cikin Najeriya mai makwabtaka da tafkin Chadi, sai kuma Gamdu a Najeriya, da ke yankin iyaka da kasar Kamaru, sannan da wata cibiya a garin Mora da ke kasar Kamaru a yankin Arewa mai nisa kusa da dajin Sambisa.