1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Margaret Ekpo, ta kasance ja gaba a siyasar mata a Najeriya

Ahmed Salisu USU
July 25, 2018

Margaret Ekpo mace jajirtacciya mai bayyana ra'ayinta, ta bude idanun mata sun fito an fafata da su a fagen kare hakkinsu da shiga siyasa. Ta taimaka wajen sauya siyasar Najeriya a lokacin da maza suka mamaye al’amura.

https://p.dw.com/p/2t3PK
Nigeria, Cartoons und Zeichnungen Portrait Margaret Ekpo
Hoto: Comic Republic

Yaushe ne a kuma ina Margaret Ekpo ta rayu?

Margaret Ekpo an haife ta a shekarar 1924 a garin Creek a jihar Cross River da ke Kudu maso Gabashin Najeriya, a lokacin Najeriya na karkashin mulkin mallakar Birtaniya. Lokacin mata ba su da iko na yin zabe. Ekpo ta rasu tana da shekaru 92 a duniya a shekara ta 2006 a birnin Calabar na jihar Cross River.

 

Wasu abubuwa ne suka sanya ake tunawa da Margaret Ekpo?

Ana tunawa da Ekpo musamman yadda ta rika karfafa gwiwar mata masu kudi da talakawa ta yadda za su yi fafutuka a fagen kwatar hakkinsu ta fannin tattalin arziki da siyasa. Ba ta gajiya ba a fafutukar ganin Najeriya ta samu 'yancin kanta. Ta kasance guda daga cikin mutanen da aka fara zaba a mukamin siyasa, a nan ne ta rinka fafutukar ganin mata sun nuna irin rawar da za su iya takawa a fagen siyasa.

Ta yaya Margaret Ekpo ta shiga harkokin siyasa?

A shekarun 1940 Ekpo wacce mijinta likita ne ta rika halartar taro na nuna adawa da yadda Turawan mulkin mallaka ke tafiyar ta jagorancin likitoci na gida. A shekarar 1946 ta kafa kungiyar mata 'yan kasuwa, ta yadda mata za su rika harkokinsu a kungiyance a birnin Aba na jihar Abia, inda take zaune tare da mijinta. A wannan lokacin Ekpo ta ba da gudunmawa wajen adawa da tsarin Turawan mulkin mallaka, inda ta shiga jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons, daga baya jam'iyyar ta zabi Ekpo a matsayin mamba ta musamman mai wakilcin mata a matsayin shugabanni. Bayan da Najeriya ta samu 'yancin kanta daga Birtaniya a shekarar 1960, an zabi Ekpo a matsayin 'yar majalisar wakilai daga yankin gabashi. Ta kasance mace ta farko a Aba kuma guda daga cikin mata kadan 'yan siyasa a kasar, da aka zaba a wannan matsayi.

Margaret Ekpo tun a 1945 ta shiga siyasa sannan tana matashiya

A tattaunawa da DW Etubong Essien wanda suka yi lokaci guda da Ekpo ya ce Margaret ita ce ta karfafa gwiwar mata kai tsaye suka shiga harkokin siyasa. 

"Tana da kazar-kazar ta na iya bayyana ra'ayi, a wancan lokaci, mata da dama ba sa harkokin siyasa ita ta rika karfafa musu gwiwa suka rika shiga harkokin siyasa har ma aka rika zabar su a majalisar wakilai."

A matsayinta na 'yar siyasa, Ekpo ta ci gaba da fafutuka ta ganin rayuwar mata ta inganta ta fuskar tattalin arziki da siyasa misali, ta yi kokari wajen ganin an gyara hanyoyi da ake bi zuwa kasuwa.

 

Me ya faru a lokacin?

Ekpo ta kasance 'yar siyasa da aka zaba har zuwa lokacin da aka fara yakin basasar Najeriya a shekarar 1967. A lokacin yakin, mahukunta a yankin Biafra sun daure ta tsawon shekaru uku har sai da ta kamu da rashin lafiya saboda rashin wadataccen abinci. A shekara ta 2001 shugaban Najeriya na wancan lokaci Olusegun Obasanjo ya maye sunan filin jirgin sama na birnin Calabar, birnin da ke kusa da garin Creek mahaifar Ekpo da sunanta. Saboda gudunmawar da ta bayar wajen ci-gaban Najeriya ta samu wannan karramawa. A yanzu ana kiran filin jirgin saman da sunan Margaret Ekpo International Airport.

 

Shiri na musamman na bitar tarihin Afirka, da zai rika zuwa kashi-kashi "African Roots", shirin hadin gwiwa da cibiyar Gerda Henkel.