1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan harin bom a Mubi

June 2, 2014

Gwamnatin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya, ta bayyana rashin jin dadinta game da tabarbarewar al'amuran tsaro a kasar, wanda ke kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

https://p.dw.com/p/1CAY1
Nigeria Soldaten Archiv 2013
Hoto: picture-alliance/dpa

Matsayin gwamnatin ta Adamawa dai, na zuwa ne bayan wani harin bom da ya kasance a garin Mubi dake arewacin jihar, harin da a cikin sa rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutane masu yawa.

Gwamnatin Adamawan ta bakin kakakin Gwamna Murtala Nyako Ahmad Sajoh na nuna rashin jin dadin ne ganin yadda rayukan jama'a da dukiyoyi suka salwanta ranar Lahadi a garin Mubin da almurun Lahadi sakamako tashin bom, lokacin da aka taru wurin kallon kwallo.

Babban takaicin gwamnatin dai, shi ne na ganin lokaci mai tsawo na kwanciyar hankali da aka samu a garin na Mubi da yayi fama da hare-hare a lokutan da suka gabata.

Wani abin damuwar ma da gwamnatin ke nunawa, shi ne na ganin karuwar yawan jami'an Soji dake yanzu a Mubi wanda a cewar gwamnatin da mamaki yanda irin wadannan hare-hare masu muni ke kasancewa, duk da cewar ba raina kwazo ko himmar jami'an tsaron take yi kai tsaye ba.

Fashewar bom din na garin Mubi wanda ta kasance a filin kwallon kafa, da abu ne da ake iya cewa ya tada hankalin masu sha'awar kwallon kafa, sai kuma babban bugu da kari na ganin karatowar da babbar gasar kwallon kafa ta duniya da za a yi kasar Brazil. Mr. Fidelis Jocktan, dan jarida ne mai nazarin harkokin wasanni a Yola.

Suma talakawa Ya-Ayyu Hannaasu, wannan harin ya kaisu ga bayyana abin dake zukatansu dangane da tsayuwar gwamnati musamman kan kare rayukan su su 'yan kasar da take jagoranta. Muhammad Adamu Babaji daya ne daga cikin masu bayyana wanna matsayi.

Gwamnatin Najeriya dai a kullum cewa take tana kan matakan maganta halin da tsaron kasar ke ciki, sai dai har yanzu alamu na ci gaba da bayyana gazawar ta ne kan kudujrin daya tilo da take ci gaba da tsayuwa a kansa.

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa
Edita: Umaru Aliyu