1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani dangane da sakamakon zaben majalisar dokoki a Jamus

September 23, 2013

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta fara shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati bayan nasarar da ta samu a zabe.

https://p.dw.com/p/19mjC
German Chancellor and leader of the Christian Democratic Union ( CDU) Angela Merkel, Hesse's Prime Minister Volker Bouffier (R) and CDU party secretary general Hermann Groehe (L) laugh before a CDU party board meeting in Berlin September 23, 2013, the day after the German general election. German Chancellor Angela Merkel faces the daunting prospect of persuading her centre-left rivals to keep her in power after her conservatives notched up their best election result in more than two decades but fell short of an absolute majority. REUTERS/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Kasuwannin hada hadar kudi, ba wai kawai a Jamus ba, harma da sauran kasashen Turai, na daga cikin sassan da ke mayar da martani game da sakamakon zaben kasar, wanda ya baiwa shugabar gwamnati Angela Merkel, wani sabon wa'adin mulki na tsawon shekaru hudu, kuma tuni ta fara zawarcin jam'iyyar SPD da ke rufa wa jam'iyyarta baya wajen yawan kuri'u domin kafa sabuwar gwamnati.Ta ce ta fara tuntubar shugaban jam'iyyar SPD Sigmar Gabriel. Sai dai ya nuna bukatar da a ba su lokaci har bayan babban taron jam'iyyarsa da zai gudana a ranar Jumma'ar da ke tafe. Merkel ta ce hakan ba zai rufe tuntubar wasu jam'iyyun ba.

Ta ce: "Batu na farko shi ne a yau na fara tuntubar jam'iyyar adawa mafi girma. Amma hakan ba zai hana tuntubar karin jami'iyyu ba. Kawo yanzu babu wani karin bayani da zan yi. CDU da CSU za su tattauna da juna game da matakin da za mu dauka nan gaba. Ka da kuma ku manta SPD za ta gudanar da babban taronta a ranar Jumma'a saboda dole mu jira har bayan wannan taro."

Social Democratic Party (SPD) top candidate Peer Steinbrueck and party leader Sigmar Gabriel (R) speak at a news conference at the SPD headquarters in Berlin, September 23, 2013. Germany's Angela Merkel began trying to persuade her centre-left rivals to keep her in power on Monday after her conservatives notched up their best election result in more than two decades but fell short of an absolute majority. REUTERS/Ralph Orlowski (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Peer Steinbrück da Sigmar Gabriel na jam'iyyar SPDHoto: Reuters

Dalilin kulla kawance da SPD

Hakan ya faru ne kasancewar, jam'iyyar FDP da ke kawance da CDU wajen kafa gwamnatin da ke gadon mulki, ta gaza samun nasarar da take bukata a wannan zaben, lamarin da masana ke cewar, na da nasaba ne da gazawarta wajen kyautata harkokin kasuwanci - kamar yadda yake a cikin manufofinta.

Joachim Scheide, masanin harkokin kasuwanci da na tattalin arziki da ke jami'ar Kiel a nan Jamus, ya ce akwai bukatar jam'iyyar ta FDP ta sake lale:

Ya ce " Na yi amannar cewar, wannan asara ce, amma kuma tilas a san da cewar, jam'iyyar FDP ba ta taka rawar da ta kamace ta ba ta fuskar samar da sauye sauyen da suka shafi hada hadar kasuwanci a cikin manufofin gwamnati. Saboda haka ne kuma masu jefa kuri'a suka ladabtar dasu."

German Economy Minister and leader of the liberal Free Democratic Party (FDP) Philipp Roesler reacts during a news conference after a presidium meeting in Berlin September 23, 2013, a day after the German general election (Bundestagswahl). REUTERS/Wolfgang Rattay (GERMANY - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Philipp Rösler na jam'iyyar FDPHoto: Reuters

Sauyin shugabanci a jam'iyyar FDP

Darasin da jam'iyyar ta FDP ta koya ne dai yasa Phillip Roesler, ministan tattalin arziki a Jamus, yin murabus daga shugabancinta, kuma tuni Christian Lindner, da ke shugabantar jam'iyyar a jihar North Rhine Westphalia ya bayyana shirye shiryen neman jan akalarta, domin ceto jam'iyyar daga halin da ta tsinci kanta a ciki. Lindner, ya ce abin da ya rage musu a yanzu, shi ne sake daura damara, ganin cewar, jam'iyyar ta FDP, rabon da ta tafka irin wannan asarar, tun a shekara ta 1949:

"A zahiri dai bamu biya bukatun masu zabe ba a lokacin da muke cikin gwamnati. Ina ganin abin ma ya kara yin muni. Ina da kwarin gwiwar cewar, da akwai mutane da yawa a Jamus wadanda ke bukatar wata jam'iyya da za ta yi sassauci wajen game manufofin tattalin arziki da na zamantakewa."

A yanzu dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta tabbatar da cewar, babu wani sauyin da za ta samar a sabon wa'adin mulkinta dangane da manufofin da suka shafi gungun kasashen Turai da ke yin amfani da takardar kudin Euro, domin kuwa a cewarta nasarar da ta samu, manuniya ce ga yakinin da masu jefa kuri'a ke dashi dangane da muradun Jamus a cikin Kungiyar Tarayyar Turai, da kuma harkokin da suka shafi duniya baki daya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal