1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaGhana

Ghana: Martani kan dokar hana auren jinsi

February 29, 2024

Majalisar dokokin Ghana ta rattaba hannu kan kudirin dokar haramta auren jinsi, kana ta ce duk wata alaqa ko ma rajin kare hakkokinsu na cikin laifukan da dokokin kasar suka haramta.

https://p.dw.com/p/4d2hF
Ghana | Nana Akufo-Addo | Doka | Auren Jinsi | Majalisar Dokoki
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-AddoHoto: Michael Kappeler/dpa

Dokar dai ta na nuni da cewa duk wanda aka samu da aikata ko yin alaqa da ma su auren jinsin ko fafutukar tallata su ko ba su kariya, zai iya fuskantar zaman kaso tsawon watanni shida ko shekaru uku zuwa biyar. Abin da ake zaman jira kamin dokar ta fara aiki shi ne sa hannun shugaban kasar. Da ta ke mayar da martani kan dokar, Farfesa Audrey Gaddepko ta jami'ar Ghana ta yi tir da saka hannun da majalisar dokokin kasar ta yi a kan kudirin dokar. Sai dai yayin da Farfesa Gadjekpo ke nuna adawarta karara da wannan doka, wasu ma su sharhin na ganin kamata ya yi shugaban kasar ya yi taka tsan-tsan. Shi kuwa Abdrahman Baba Alhaji ya ce kasancewar wannan dokar ba wani hurumi ba ne na cin zarafi, kamar yadda a wakwanakin baya-bayan nan a kan shiga filayen taro da tsumagiya ana bulale mutane. Kawo yanzu dai shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo bai bayar da tabbacin abin da za a tsammata ba daga gare shi dangane da batun sahalewar tasa.