1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan harin minista a kasar Masar

September 6, 2013

'Yan adawa da ke ci-gaba da nuna rashin goyon bayansu ga juyin mulkin da soji suka yi a Masar sun nuna rashin amincewarsu da harin da aka kai wa ministan cikin gidan kasar.

https://p.dw.com/p/19csw
epa03851709 Security officials inspect the scene of a bomb blast targeting Egyptian Interior Minister Mohammed Ibrahim near his home in Nasr City, Cairo, Egypt, 05 September 2013. Egyptian Interior Minister Mohammed Ibrahim survived an assassination attempt involving bombs set off near his motorcade. It was the first such attack in Egypt in years. EPA/KHALED ELFIQI
Kairo Anschlag auf Innenminister Ibrahim 05.09.2013Hoto: picture-alliance/dpa

Gamayyar masu adawa da juyin mulkin da sojie suka yi a Masar sun yi Allah wadai da harin da aka kai wa ministan cikin gidan kasar Mohammed Ibrahim jiya Alhamis, inda suka ce gwamnati za ta iya amfani da harin wajen ci-gaba da matsin lamba ga masu adawa da ita. Gamayyar dai ta bayyana hakan ne gabannin wata zanga-zanga da ta kira a yi a wannan Jumma'ar don ci-gaba da nuna fushinta da hambara da gwamantin farar hular kasar wanda Mohammed Morsi na jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ta jagoranta.

Shi ma dai shugaban rikon kwaryar kasar Adli Mansur Hadi ya nuna rashin jin dadinsa dangane da wannan hari na jiya kan ministan nasa na cikin gida inda ya ce abu ne da hukumomin kasar ba za su lamuta ba. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta fito fili ta ce ita ce ta kai harin da ma dalilinta na yin hakan. Sai dai 'yan sanda sun ce suna nan suna bincike.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal