1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan hukuncin kisa a Edo

Usman ShehuJune 25, 2013

Daga ciki da wajen Najeriya ana mai da martani kan rataye mutane a jahar Edon Najeriya.

https://p.dw.com/p/18wVA
Ein nachgebauter Galgen steht am Freitag (19.02.2010) im Eingangsbereich des Neanderthal Museums in Mettmann. Er gehört zu der Sonderaustellung "Galgen, Rad und Scheiterhaufen", die bis zum 27. Juni 2010 Einblicke in den gruseligen Leistungskatalog der Strafen und seine Orte im 17. Jahrhundert gibt. Foto: Roland Weihrauch dpa/lnw (zu KORR:" Henker, Beil und Galgen - Museum zeigt das Grauen")
Alamar rataye mutaneHoto: picture-alliance/dpa

A jiya ne aka aiwatar da hukuncin kisa ta rataya kan wasu mutane hudu da wata kotu ta tabbatar da laifinsu na fashi da makami a jahar Edo a tarayyar Najeriya,lamarin kuma da ke ci gaba da jan hankulan kungiyoyin fafutukar yancin dan adam,musamman ma na kasa da kasa.

Gwamnatin jahar Edo da ke yankin Niger Delta, ta tabbatar da cewa a daren Talatan da ta gabata, ta umarci zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya na wasu 'yan fashi da makami su hudu da wata kotun ƙoli a ƙasar ta same su da laifi, inda kuma yanzu akwai wani ƙarin ragowar ɗaya dake dakon tasa ratayar.

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Majalisar dokokin Tarayyar NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Kwamishinan shari'a a jahar ta Edo, Henry Idahogan ya tabbatar da kisan na mutanen huɗu, matakin kuma da aka nunar cewar shine irinsa na farko a kasar tun shekara ta 2006, da kuma yanzu ke fuskantar suka na ƙungiyoyi masu fafutukar yanci ɗan Adam. Mr Peter Okhiria shine kakakin gwamnan jahar ta Edo, ga kuma abinda ya shaida wa wakilinmu Muhammed Bello ta wayar tarho.

"Gwamna ya sa hannu a umarnin wannan kisa tun shekarar da ta gabata, ba wai ɗon shugaban ƙasa ya yi magana bane kamar yadda wasu ke tunani. Kuma sukar da ƙungiyar kare yancin ɗan Adam, ta Amnesty International ke yi kan wannan mataki, ba wani sabon abu bane, amma in akai la'akkari da yadda masu laifi irinsu ke ɗaukar rayukan jama'ar mu ba gaira ba sabar, to akwai doka ta kasarmu, wadda za ta hau kansu, kuma abinda gwamna ya yi, dama ce da dokar ƙasa ta ba shi"

Symbolbild Amnesty International und Human Rights Watch gegen Hinrichtung von Jugendlichen Copyright: DW/AP
Alamar gyamar da Amensty International ke yi kan hukuncin kisaHoto: AP/DW

Tun dai kafin ƙaddamar da kisan, ƙungiyar kare yancin ɗan Adam, wato ta Amnesty International ,tace ta nemi da hukumomi a Najeriyar da su jinkirta zartar da hukuncin, dan haka ƙungiyar ta yi tur da abinda ta ce rashin mutunta haƙƙin ɗan Adam ne karara da daman ya yi katutu a ƙasar.

Titel: DW_Nigeria_Integration2 Schlagworte: Nigeria, Präsident, Goodluck Jonathan Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 04. April 2011 Aufnahmeort: Abuja, Nigeria Bildbeschreibung: Präsident Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck JonathanHoto: Katrin Gänsler

Wani Mr Izik Isuku da ke lura da al'ammura a ƙasar yace "Haƙiƙa Najeriya ta shiga jerin ƙasashen duniya da suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar martaba rai na ɗan Adam, to amma in idan ka yi la'akari da munin aikata muggan laifuka irin na fashi da makami, inda sau tari 'yan fashin kan yi kisa da fyaɗe, ni ina ganin a yanayin da muke a ƙasar a yanzu, hukuncin kisan ya yi dai dai"

Ba dai tun yanzu bane ake ta kokawa kan yadda gidajen yari a ƙasar ta Najeriya ke fama da cunkoso da kuma musamman zargin cewar siyasa ma ta na samun gindin zama a harkokin shari'a a ƙasar.

Mawallafi: Muhammad Bello

Edita:     Usman Shehu Usman