1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Iyalan Mandela kan ta'aziyyar da ake musu

December 7, 2013

Iyalai da 'yanuwan Nelson Mandela sun mika sakon godiyarsu dangane da sakonni na alhini da ta'aziyya da suke cigaba da samu daga kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/1AUqj
Marigayi Nelson Mandela
Hoto: Picture-Alliance/Photoshot

Mai magana da yawun iyalan tsohon shugaban na Afirka ta Kudu Temba Matanzima ne yai magana a madadin iyalan Mandelan a Johannesburg inda ya ce sun yi rashin uban wanda ke zaman fitila da ke haskaka musu lamuransu tare da sanya su kan tafarki madaidaici.

Mr. Matanzima ya ce wannan rashi da suka yi na Madiba ba wai su kadai ya shafa ba har ma da kasar da ma duniya baki daya, duba da irin rawar da ya taka wajen ganin jama'a a kasar sun kasance tsintsiya madaurinki daya.

A daura da wannan kuma, gwamantin Afirka ta Kudu na cigaba da gudanar da shirye-shirye na jana'aizar Nelson Mandela inda hukumomin suka ce za a shafe kwana uku cikin makon gobe ana ratsawa da gawarsa ta titunan Pretoria, babban birnin kasar don baiwa jama'a damar yin ban kwana da shi.

A bisa wannan ne ma gwamnatin shugaba Jacob Zuma ta umarci al'ummar birnin na Pretoria da na sauran yankunan kasar da za su isa birnin da su yi layi kan titunan birnin yayin da ake wucewa da gawar don gimama shi, kazalika gwamnatin ta ce za a ajiye gawar a tsawon wadannan kwanaki a ginin Union Bulding da ke birnin don jama'a su gani sai dai ba za a bari a dau hotuna ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe