1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta mayar da martani da kakkausan lafazi

Abdoulaye Mamane Amadou
September 19, 2021

Hukumomin Mali sun mayar da martani da kakkausan lafazi kan kasashen da ke zarginsu da neman kulla yarjejeniyar tsaro don dauko sojojin hayar Wagner daga Rasha.

https://p.dw.com/p/40XRs
Mali | Übergangs-Ministerpräsidenten Choguel Kokalla Maïga
Choguel Kokalla MaïgaHoto: Kommunikationsdienst des Premierministers

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Lahadi, ma'aikatar harkokin wajen Mali ta ce kasar na da 'yancinta na tattaunawa da duk wani da take ganin zai kaita ga tabbatar da tsaro da doka da oda.

Sai dai duk da yake bata fito fili ta ambaci wata kasar ba, sanarwar ta kuma kara da cewa ba wata kasar da za ta zabar wa Mali abokiyar dasawa ko hulda. Ko a yayin wata ganawa da manela labarai a baya firaministan gwamnatin wucin gadin kasar ta Mali Choguel Kokalla Maïga cewa ya yi kasar na da hurumin yin abinda taga dama.

"Ba za a hana mu sayen kayan aiki daga wata kasar da muke da hulda da ita ba, hakan kuma ba wani da zai hana mu aika mutanenmu karo ilimi ko horo a wata kasar da muke da hulda ita don dai kawai wata kasar bata shiri da ita."

 Kasashen Jamus da Faransa da ma kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, sun yi kakkausar suka kan matakin kasar Mali na kulla yarjejeniyar tsaro da wani kamfanin sojojin haya mai suna Wagner na kasar Rasha, suna masu cewa matakin ka iya dagula al'amura a Mali da ma yankin yammacin Afirka.