1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Abuja ta fusata da rusa ofishin jakadancinta

Uwais Abubakar Idris AMA
June 22, 2020

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani mai zafi a game da rushe wani sashi na ofishin jakadancinta a Ghana tare da bukatar kasar ta hanzarta daukan matakin gyara a cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/3eAIX
Guinea-Bissau Delegation ECOWAS
Geoffrey Onyeama ministan harkokin wajen NajeriyaHoto: DW/B. Darame

Mahukuntan Najeriyar sun harzuka kan abinda ya faru a wani sashi na ofishin jakadancin Najeriyar da ke birnin Accra kasar Ghana biyo bayan da ‘yan bindiga suka afkawa sashin ofishin suka tare da rusa shi. Ministan kula da harkokin kasashen wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama yace dole ne an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya "Ya ce Najeriya ta aika da samaci ga da kiran jakadan kasar Ghana a Najeriya domin bayyana bacin ran Najeriya kan lamarin, sai dai har yanzu ba su samu wani sako daga mahukuntan Ghana kan batun ba". Masu sharhi da nazari kan harkokin huldar kasashen biyu na bayyana cewa hakan ya sabawa kudurin diplomasiyya na 22 da aka rattaba hannu kansa a Vienna a kan duk wani gini na ofishin jakadancin wata kasa da ke a wata kasar, to amma sai dai ana ganin cewa da alamun akwai wata rashin jituwa ta fanin dimplomasiyya tsakanin Najeriya da Ghana, duba da yadda a baya bayan nan ake samun sabani kan batutuwa da suka shafi dimplomasiya kamar zargin korar ‘yan Najeriya har zuwa ga rushe wani sashi na ofishin jakadancin Najeriya a Ghana, ko da yake gwamnatin Najeriya ta karyata.Tuni majalisar dokokin Najeriya ta bayyana cewa tura ta fara kaiwa bango kan al’amari na diplomasiya tsakanin kasashen biyu.