1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Uganda akan somalia

November 18, 2006
https://p.dw.com/p/BubN

Gwamnatin Uganda tace zata gabatarwa Mdd kokenta,adangane da zaiginda ake mata da wasu kasashe guda 9,na sayen makamai domin aikawa bangarorin adawa a kasar somalia dake fama da rigingimu.Ministan tsaron Uganda Chrispus Koyonga ya fadawa manema labaru a birnin Kampala cewa ,wannan maganace da bata da tushe ,kuma adangane da hakane kasarsa ke shirin gabatarwa mdd kokenta.Mr Koyonga dai yana mayar da martani ne adangane da wani rahoto,na wani komitin bincike na mdd ,dake zargin kasar Uganda da Habasha ,amatsayin kasashen dake sayen kayayyakin fada da samarda jamiai wa gwamnatin jeka nayika na somaliyan,adangane da rikicinta da kungiyoyin musulmin kasar dake da madafan iko a birnin Mogadishu.Ayayinda rahotan ya zargi kasashen da suka hadar da Libya da Yemen wajen marawa kungiyoyin baya.A jiya nedai Libya ta mayar da martanin,karyata wannan zargi da ake mata,inda tace tasha kasancewa mai shiga tsakani wajen warware rigingimu a somaliyan ,tsakanin bangarorin dake adawa da juna.