1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Najeriya a kan canji sheƙa na Siyasa

Umaru AliyuJanuary 30, 2014

'Yan siyasa da talakawan Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu bayan da tsoffin gwamnonin kuma ‘yan Majalisun dattawa suka fice daga jam'iyyar PDP da ke yin mulki zuwa APC mai adawa.

https://p.dw.com/p/1AzkO
Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

Tun bayan da jam'iyyar APC ta fitar da sanarwa da ke nuna cewar wasu Sanatoci 11 sun bar jam'iyyar su ta PDP tare da komawa jam'iyyar APC ‘yan Najeriya ke tattaunawa gami da yin muhawarori musamman a wuraren zaman al'umma.

Ra'ayoyin al'umma dangane da canji sheƙarRa'ayoyin al'ummar sun banbanta kan wannan sauya sheƙa inda wasu suka yi marhabin da matakin da ‘yan Majalisar dattawan suka ɗauka wasu kuma na cewar abin takaci ne kuma ma Allah ya raka taki gona. Alh Lamido Umar Chikaire wanda ya ce shi ɗan jam'iyyar PDP ne yana maraba da fitar waɗannan 'yan majalisa.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Ya ce :''Wannan ra'ayi nasa shi ne na yawancin magoya bayan jam'iyyar PDP mai mulki da suke ganin yanzu jam'iyyar su za ta gyaru da fitar masu komawa jam'iyyar APC.'' Sanatoci kamar Garba Saleh na ganin duk masu adawa da fitar su jam'iyyar PDP ba ya son ci gaba talakawa suke yi ba. Sai dai wasu mutane da na tattauna su sun yarda da cewa wannan sauya sheƙar a wannan lokaci ba abu ne da ba zai haifar da alheri. Wannan kuma shi ne ra'ayin Malam Jauro Hammadu wani mai yin fashin baƙi kan harkokin siyasa a Tarayyar Najeriya. Masana kimiyyar siyasa dai na ganin yakamata talakawa su nitsu tare da tattara hankulan su waje ɗaya su yi dogon nazari musamman ganin ana tinkarar manyan zaɓuɓɓuka na ƙasa a shekara ta 2015.

Mawallafi : Alamin Suleiman Mohammed
Edita : Abdourahamane Hassane