1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masaƙu a ƙasar Bangladesh na shirin bada kai

November 14, 2013

Yayinda boren ma'aikata a kamfanonin saƙa a ƙasar ya kassara aikin saƙa, yanzu kamfanonin sun fara sauraron buƙatunsu na ƙara albashi

https://p.dw.com/p/1AHLs
Workers shout slogans as they protest against the death of their colleagues after a devastating fire in a garment factory which killed more than 100 people, in Savar November 26, 2012. Thousands of angry textile workers demonstrated in the outskirts of Dhaka on Monday after a fire swept through a garment workshop at the weekend, killing more than 100 people in Bangladesh's worst-ever factory blaze. REUTERS/Andrew Biraj (BANGLADESH - Tags: DISASTER BUSINESS TEXTILE EMPLOYMENT CIVIL UNREST)
Ma'aikatan masaku ke zanga-zanga a DhakaHoto: Reuters

An sake buɗe masaƙu a ƙasar Bangaladesh bayan zanga-zangar da ma'aikata suka yi bisa neman ƙarin albashi. Dama dai sama da masuƙu 200 ne suka rufe aikinsu, kafin Firaministar ƙasar Sheikh Hasina ta shiga tsakani. Wasu kamfanonin da suka gana da Firaministar, sun amince su yi wa ma'aikatan ƙarin albashi na kashi 77 cikin ɗari, inda yanzu albashin lebura ya kai dalar Amirka 66 a wata, wato kwatankwacin Naira dubu goma kacal. Gwamnatin ƙasar dai ta kafa kwamitin da ya amince da wannan ƙaramin albashin, amma shi ma wasu kamfanonin sun ƙi biya, Duk da cewa ƙasar ita ce mafi ƙanƙantan albashi a duniya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh