1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin kasa ya yi sanadiyar mutuwar mutum 25

Ramatu Garba Baba
February 27, 2019

Mutum akalla 25 ne suka mutu wasu fiye da 50 suka sami rauni a sanadiyar hadarin jirgin kasa a birnin Alkhahira a wannan Laraba, a yayin da hukumomi ke bincike ko harin ta'addanci ne aka kai wa kasar.

https://p.dw.com/p/3ECIk
Ägypten Zug Absturz November 2013
Hoto: Picture-alliance/dpa

Jirgin dai ya saki hanya kafin ya daki wani shinge da ke tashar jirgin, bayan nan an yi ta jin fashewa da hayaki da ya turnuke iska. Lamarin ya haifar da rudani. A jawabin Firaiministan kasar Mostafa Mad-bouly,  jim kadan bayan aukuwar lamarin, ya ce za su gudanar da bincike kuma za a hukunta duk wani wanda ke da hannu in har an tabbatar an kitsa hadarin ne da gangan. Babu dai tabbaci daga hukumomi ko yana da nasaba da ayyukan ta'addanci.

Yanzu haka kuwa rahotannin da ke shigo mana daga kasar Mali na nuni da cewa, mutum akalla goma sha bakwai sun mutu a wani cunkoson jama'a.