1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta kafa komitin da zai tsara sabon kundin tsarin mulki

July 21, 2013

Shugaban wucin gadin Masar, Mansur al Adly ya nada wani komitin kwararru da zai yi nazari a kan kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/19BUw
Hoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Ofishin shugaban da ke birnin Alkahira ya ce a ranar Lahadi ne mambobin komitin da suka hada da manyan malaman jami'a hudu da alkalai shida suka kama aiki. Kenan wajibi ne shugaban na rkion kwarya ya shirya zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin, nan da watannin hudu.Sojoji ne suka soke kundin tsarin mulkin, bayan da suka tubuke tsohon shugaba. Mohammed Mursi a ranar uku ga watan Yuli. Da kashi 63 daga cikin dari na sakamakon kuri'ar raba gardama da aka kada a watan Disamban 2012 ne aka tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar.

Ita dai gwamnatin Masar tana kokari ne ta daidata al'amura a kasar ta arewacin Afirka da ke fama da yawaitar arangama tsakanin magoya bayan Mursi da masu adawa da shi. Mutane kusan dari ne dai suka rasa rayukansu a cikin rikicin da ya barke bayan hambarar da Mursin.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu