1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi Masar domin shirya AFCON ta 2019

Gazali Abdou Tasawa MAB
January 8, 2019

Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta zabi kasar Masar domin daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta shekara ta 2019 domin maye gurbin kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/3BC6C
Afrika-Cup Pokal
Hoto: picture alliance/dpa/N. Bothma

Shugaban hukumar ta CAF Ahmad Ahmad ne ya sanar da hakan a wannan Talata a karshen kuri'ar da kwamitin zartarwa na hukumar ta CAF ya shirya tsakanin kasar ta Masar da Afirka ta Kudu a wannan Talata a birnin Dakar na Senegal.

Kasashen na Masar da Afirka ta Kudu sun kawo daukin daukar nauyin gasar ta 2019 ne bayan da hukumar ta karbe daga hannun kasar Kamaru a bisa jinkiri wajen kammala gina filayen wasanni da wuraren karbar baki da kuma matsalar tsaro da kasar ke fama da ita a sakamakon hare-haren Boko Haram da kuma rikicin 'yan awaren yankin da ke magana da Turancin Ingilishi.

Za a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar ta Afirka daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin wannan shekara ta 2019.