1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maslaha ga rikicin Yukren

December 9, 2013

Kungiyar Tarayyar Turai na kokarin warware rikicin siyasar kasar Yukren

https://p.dw.com/p/1AVgC
Ukraine Proteste 09.12.2013
Hoto: Sergei Supinsky/AFP/Getty Images

Kantomar kula da manufofin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Catherin Ashton ta bayyana cewar, a wannan Talatar (10.12.13) ce za ta kai ziyarar kwanaki biyu zuwa kasar Yukren, bayan da dubun dubatan masu zanga zanga suka fito titunan kasar domin nuna adawarsu da matakin da shugaban kasar ya dauka na kin sanya hannu akan yarjejerniyar kasuwanci tare da Kungiyar Tarayyar Turai. Wata sanarwar da Hukumar Tarayyar Turai ta fitar, ta ce kantomar na sa ran ganawa da daukacin masu ruwa da tsaki cikin rikicin siyasar kasar ta Yukren daga sassan biyu, da kuma kungiyoyin fararen hula. Masu boren dai sun fara zanga zangar ce tun bayan da shugaba Yanukovich ya ki sanya hannu akan yarjejeniya tare da Turai, inda ya gwammace kyautata huldar kasuwancinsa tare da kasar Rasha.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu