1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu neman mafaka aTurai 17 sun rasu a teku

December 5, 2014

Dubban 'yan gudun hijira ne dai ke rasa rayukansu a kan hanyar zuwa Turai ko ta halin kaka. Ministan harkokin wajen kasar Italiya ya ce an gano su a karkashin jirgin ruwa.

https://p.dw.com/p/1DzqM
Flüchtlinge Lampedusa
Hoto: picture alliance / ROPI

Wata jaridar kasar Italiya ta bada rahoton cewa masu aikin ceto sun gano wasu gawarwaki 17 a teku, bayan da jirginsu ya baro kasar Libya. karon farko da aka samu rahoton gano wasu matattu tun bayan da Kungiyar Tarayyar Turai ta karbi aikin ceto a yankin Meditareniya.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Paolo Gentiloni ya bayyana cewa, an gano jirgin ne da ga tazarar nesan mil 150 nesa daga tsibirin Lampedusa, inda ya kasance mil arba'in daga birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar ta Libya. Gentiloni ya ce kasar ta Italiya za ta shiga aikin bincike cikin lamarin.

Ayyukan masu bincike da ceto daga kungiyar ta EU na gudanar da sintiri ne dai da tazarar mil talatin daga gabar tekun kasar ta Italiya.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Usman Shehu Usman