1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zanga-zanga sun yi kira da sako ´yan jarida da aka kame a Nijer

October 20, 2007
https://p.dw.com/p/Bu87

Masu zanga-zangar lumana a birnin Yamai na janhuriyar Nijer a wani taron gangami wanda hadin guiwar kafofin watsa labaru masu zaman kansu tare da kungiyoyin kwadago na kasar suka shirya sun yi Allah wadai da irin bita da kulli da hukumomin kasar ke yiwa ma´aikatan kafofin watsa labaru. Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da alluna wadanda suka yi rubuce rubuce na yin tir da irin kuntatawa ´yan jarida da hukumomi ke yi da kuma sako ´yan jaridar nan biyu dake tsare wato Musa Kaka wakilin gidan radiyon Faransa da kuma Ibrahim Manzo Diallo editan mujallar nan da ake kira Air-Info. Nan gaba a cikin shirin mu na wannan lokacin zamu kawo muku karin bayani kan yadda zanga-zangar ta gudana.