1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata a Afrika suka fi kamuwa da cutar kanjamau

Hauwa Abubakar AjejeDecember 7, 2005

Baya ga yadda halittarsu take,matsalolin halin rayuwa da batun al ada,suna taka rawa wajen yada cutar tsakanin mata a Afrika

https://p.dw.com/p/Bu3a
Hoto: AP

Wakiliyar Afrika ta kudu mai bada shawara akan cutar kanjamau a asusun kula da yawan jamaa na Majalisar Dinkin Duniya, Helen Jackson tace kusan kashi 60 cikin dari na wadanda suke dauke da cutar kanjamau mata ne,kuma yawncinsu matasa.

Tace bayanai sun nuna cewa mata sune suka fi kamuwa da cutar kusan ninki biyu fiye da maza.

A cewar Michel Sidebe,mataimakiyar darektan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya wadda ta kunshi kungiyoyi 10 masu yaki da cutar,matan Afrika kuwa sune abin ya fi shafa,domin kuwa cikin dukkannin mata da suke dauke da cutar a duniya kashi 77 cikin dari cikinsu, matan Afrika ne.

A kasar Afrika ta kudu,yan mata masu shekaru daga 15 zuwa 24,suke cikin hadarin kamuwa da cutar ninki uku fiye da maza tsararrakinsu.

Baya ga yadda halittarsu take sanya saurin kamuwa da cutar,akwai kuma batutuwan halin rayuwa da alada da suke taka babbar rawa wajen yadawa mata cutar a nahiyar Afrika.

Taron yace, mata da suke dogara kacokam da dukiyar mazajensu,suna tsoron fadawa mazajen nasu yin anfani da kororon roba koda kuwa sun tabbatar cewa mazajen suna dauke da cutar ta kanjamau.

Wani bincike da hukumar yaki da cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a farkon wannan wata,ya nuna irin hadarin da mata suke ciki na saurin kamuwa da cutar kanjamau koda kuwa sun kasance tare da miji guda har iyaka rayuwarsu.

Rahoton yace,cikin mata da aka yi bincike akansu a garuruwan Harare na kasar Zimbabwe da Durban da Soweto a Afrika ta kudu,kashi 66 cikin dari na matan sunce sun kasance tare da mazajensu ne tun lokacin da sukayi aure,kashi 79 kuma sunce basu sadu da namiji ba har sai da suka kai shekara 17,amma duk da haka kashi 40 daga cikinsu suna dauke da kwayar cutar ta HIV.

Helen Jackson tace,a wasu lokutan mata da suke dauke da cutar musamman a yankunan karkara,dole ne su nemi iznin mazajensu kafin su fara neman maganin cutar.

Tace ga kuma nauyin kula da marasa lafiya ko kuma masu dauke da cutar da ya rataya a wuyan matan da kuma samarda abinci ga iyali,musamman idan maigida ne yake da cutar ta kanjamau.

Hakazalika matan suna iya yada cutar ga jariransu a lokacin haihuwa ko yayin shan mama,Helen tace bugu da kari kuma su matan ake dorawa laifin daukowa iyali wannan cutar.

Shugaban shirin,Peter Piot,yace a halin yanzu kasashen duniya da kungiyoyi sun farga da irin nauyi dake kan mata na Afrika,kuma ana nan ana ci gaba da tattaunawa akan batun bambamcin jinsi tsakanin kungiyoyi da ada basa son tabo wannan batun,hakazalika matan a cewar Helen Jackson sun fara bude baki suna fadin abinda yake damunsu cikin alumma.